Daruruwan 'yan Kwankwasiyya sun yi mubayi'a ga APC a jihar Jigawa

Daruruwan 'yan Kwankwasiyya sun yi mubayi'a ga APC a jihar Jigawa

Yayin da lamurran siyasa a kasar Najeriya ke cigaba da zafafa musamman ma bayan sauya shekar tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata dake wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso daga APC zuwa PDP abubuwa ke ta wakana.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne ma kuma muka samu labarin cewa wasu mabiya darikar Kwankwasiyyar a jihar Jigawa suka cire jajayen hulunun su tare da yin mubayi'a ga jam'iyyar ta APC.

Daruruwan 'yan Kwankwasiyya sun yi mubayi'a ga APC a jihar Jigawa
Daruruwan 'yan Kwankwasiyya sun yi mubayi'a ga APC a jihar Jigawa

KU KARANTA: Wani matashi ya fallasa yadda suke kashe fulani a Taraba

Legit.ng ta samu cewa Kwamishinan kudi na jihar ta Jigawa Honorabul Namadi Kafin Hausa ne ya jagoranci karbar tubabbun 'yan darikar ta Kwankwasiya a garin Hadejia.

A wani labarin kuma, Dan majalisar nan dake wakiltar mazabar Kiru da Bebeji a majalisar wakilan Najeriya Honarabul Abdulmumini Jibrin ya yi ikirarin cewa ba bu wani mahalukin da zai iya kada Shugaba Buhari a zaben 2019 mai zuwa.

Honarabul Jibrin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake fira da manema labarai a garin Abuja, babban birnin tarayyar inda yace idan akayi la'akari dukkanin masu hankoron kalubalantar Shugaba Buhari din babu wanda ya kai shi dumbin masoya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng