Anfani 5 da 'ya'yan iccen dinya keyi a rayuwar bil'adama

Anfani 5 da 'ya'yan iccen dinya keyi a rayuwar bil'adama

Kamar yadda muka saba daga lokaci zuwa lokaci mukan zakulo maku yanyoyin da zaku kara samun lafiyar jikunnan ku musamman ma ta hanyar anfani da abubuwan dake zagaye da mu.

Yau ma kuma gamu dauke da alfanun 'ya'yan iccen nan bakake na dinya da kan nuna musamman ma a irin wannan lokacin na tsakiyar damina.

Anfani 5 da 'ya'yan iccen dinya keyi a rayuwar bil'adama
Anfani 5 da 'ya'yan iccen dinya keyi a rayuwar bil'adama

KU KARANTA: Sheikh Pantami yayi magana game da aminin sa da aka sace

Dinya dai da ake kira da Black plump juice a turance icce ne da kan fito a gonakin mutane kuma tana yin girma sosai sannan kuma tana fitar da bakaken 'ya'ya a tare da ita dake kama da na kanya.

Legit.ng ta zakulo maku muhimman alfanun ta 5 a jikin dan adam domin anfanin ku:

1. Tana taimakawa wajen gyaran ciki da muka maganin matsalolin da ke tattare da hakan kamar gudawa.

2. Tana maganin cuwalwatan da suka shafin hakora da ma baki gaba daya.

3. Tana maganin dankanoma da basir mai tsiro.

4. Tana maganin tari da kuma cutar Asuma.

5. Tana maganin mura da kuma karin karfin garkuwar jiki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel