Ina iya barin jam’iyyar APC – Gwamnan jihar Kwara
Bayan kiraye-kiraye daga masu ruwa da tsaki a jihar Kwara, gwamnan jihar, Dr Abdulfatah Ahmed ya yi Karin haske cewa yana iya barin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Gwamnan ya bayyana cewa jam’iyyar bata kai yadda mutanen jihar Kwara suka zata ba.
Gwamna Ahmed ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Yuli a dakin taron jihar, Ilorin yayinda yake aida artani ga bukatun masu ruwa da tsaki a yankin Kwara ta tsakiya, da suka bukaci shi da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da su bar APC.
KU KARANTA KUMA: Fashin Offa: ‘Yan sanda masu bincike sun biyo Saraki har Ofis
Ya ce shugabannin APC sun ki magance lamuran dake tasowa a jam’iyyar.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ya yi imani da shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Sanatan yayi magana ne bayan sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun gana da shugaban kasar a ranar Laraba, 25 ga watan Yuli.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng