'Yan Boko Haram sun kashe mutane 18, sun kuma sace mata 9 a yankin Chadi

'Yan Boko Haram sun kashe mutane 18, sun kuma sace mata 9 a yankin Chadi

Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe manoma 18 tare da sace mata guda 9 a wani yanki na kasar Chadi

'Yan Boko Haram sun kashe mutane 18, sun kuma sace mata 9 a yankin Chadi
'Yan Boko Haram sun kashe mutane 18, sun kuma sace mata 9 a yankin Chadi

Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe manoma 18 tare da sace mata guda 9 a wani yanki na kasar Chadi. Gwamna Mahamat Saleh shine ya sanarwa da manema labarai cewar 'yan ta'addar sun shigo Kauyen Mayerom dake yankin Tafkin Chadi da daddare, inda suka dinga yiwa manoman yankan rago.

DUBA WANNAN: An kama wanda ya kashe Diyar tsohon mataimakin gwamnan Ondo

Ya ce 'yan ta'addan sun sace mata guda tara, amma a cikin su an samu wacce ta samu nasarar kufcewa daga hannun su.

"Manoman sun shiga wani yanki domin neman wurin noma, wurin kuma an jima da hana shiga saboda matsalar tsaro dake tattare da wurin, shigar su keda wuya 'yan ta'addar suka far musu," inji shi.

'Yan ta'addar Boko Haram dai sun shafe kusan shekaru 9 suna kokarin kafa daular musulunci a yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda dalilin hakan ne matsalar take shafar kasashe da suke makwabtaka da Najeriyan irin su kasar Chadi, Nijar da kasar Cameroon.

Rikicin ya kashe sama da mutane 30,000 sannan ya raba sama da mutane miliyan 2.7 da muhallin su

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng