Farin jini daga Allah: Wani dan kudu ya ba Buhari zungura-zungan motocin kamfe 31 kyauta

Farin jini daga Allah: Wani dan kudu ya ba Buhari zungura-zungan motocin kamfe 31 kyauta

Kamar dai yadda muka samu labari, daya daga cikin 'yan gani-kashe nin shugaba Muhammadu Buhari a yankin kudancin Najeriya ya baiwa shugaban kasar zungura-zunguran motoci domin yayi yakin neman tazarcen sa a zaben 2019.

Masoyin dai na shugaba Buhari da har yanzu ba mu samu cikakken sunan sa ba amma dai dan asalin jihar Akwa Ibom ne dake yankin kudu maso kudancin kasar nan, kamar dai yadda muka ji.

Farin jini daga Allah: Wani dan kudu ya ba Buhari zungura-zungan motocin kamfe 31 kyauta
Farin jini daga Allah: Wani dan kudu ya ba Buhari zungura-zungan motocin kamfe 31 kyauta

KU KARANTA: "Atiku ne kadai zai iya kada Buhari a 2019"

Legit.ng ta samu cewa motocin da ya bada kirar bas-bas ne masu adadin kujeru 18 har guda 31 dake zaman adadin yawan kananan hukumomin jihar duk domin yin yakin neman zaben shugaba Buhari a shekarar 2019.

Farin jini daga Allah: Wani dan kudu ya ba Buhari zungura-zungan motocin kamfe 31 kyauta
Farin jini daga Allah: Wani dan kudu ya ba Buhari zungura-zungan motocin kamfe 31 kyauta

A wani labarin kuma, Bangaren yan aware na jam'iyya mai mulki ta Reformed-All Progressives Congress (R-APC) ta bayyyana cewa tuni fa bakin alkalami ya bushe game da maganar ficewar su daga jam'iyyar duba da irin rashin adalcin a ka yi ta yi masu a baya.

Haka zalika 'yan tawayen sun bayyana cewa duk wani dadin bakin da shugaba Muhammadu Buhari zai yi masu da cin hancin da za'a basu na mukamai ba zai sa su canza ra'ayi ba kamar dai yadda mai magana da yawun su, Kassim Afegbua ya fada.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel