Bakin alkalami ya bushe: Dadin bakin Buhari ba zai hana mu ficewa daga APC ba inji su Buba Galadima

Bakin alkalami ya bushe: Dadin bakin Buhari ba zai hana mu ficewa daga APC ba inji su Buba Galadima

Bangaren yan aware na jam'iyya mai mulki ta Reformed-All Progressives Congress (R-APC) ta bayyyana cewa tuni fa bakin alkalami ya bushe game da maganar ficewar su daga jam'iyyar duba da irin rashin adalcin a ka yi ta yi masu a baya.

Haka zalika 'yan tawayen sun bayyana cewa duk wani dadin bakin da shugaba Muhammadu Buhari zai yi masu da cin hancin da za'a basu na mukamai ba zai sa su canza ra'ayi ba kamar dai yadda mai magana da yawun su, Kassim Afegbua ya fada.

Bakin alkalami ya bushe: Dadin bakin Buhari ba zai hana mu ficewa daga APC ba inji su Buba Galadima
Bakin alkalami ya bushe: Dadin bakin Buhari ba zai hana mu ficewa daga APC ba inji su Buba Galadima

KU KARANTA: Saraki ya sha mamaki da ya ziyarci Sarkin Ilori

Legit.ng ta samu cewa ya kuma kara da cewa su fa an sha su sun warke domin kuwa ba wannan ne karo na farko ba da ake yi masu alkawari amma kuma a kasa cikawa ba don haka ba sauran dadin bakin da za'a yi masu yanzu.

A wani labarin kuma, Kamar dai yadda muka samu labari, daya daga cikin 'yan gani-kashe nin shugaba Muhammadu Buhari a yankin kudancin Najeriya ya baiwa shugaban kasar zungura-zunguran motoci domin yayi yakin neman tazarcen sa a zaben 2019.

Masoyin dai na shugaba Buhari da har yanzu ba mu samu cikakken sunan sa ba amma dai dan asalin jihar Akwa Ibom ne dake yankin kudu maso kudancin kasar nan, kamar dai yadda muka ji.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng