Sarkin Ilori ya ba Saraki mamaki da kai masa ziyara a fadar sa

Sarkin Ilori ya ba Saraki mamaki da kai masa ziyara a fadar sa

Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari ya baiwa Shugaban majalisar dattijan Najeriya Dakta Bukola Saraki mamaki lokacin da ya nadashi sarautar Wazirin masarautar Ilori ba tare da sanin shi ba.

Sarkin dai kamar yadda muka samu ya nada shi sarautar ne lokacin da ya kai masa ziyara a fadar sa a cigaba da rangadin godiya ga Allah da yake yi biyo bayan nasarar da ya samu a kotun koli akan shari'ar sa da yayi da kotun da'ar ma'aikata a kwanan baya.

Sarkin Ilori ya ba Saraki mamaki da kai masa ziyara a fadar sa
Sarkin Ilori ya ba Saraki mamaki da kai masa ziyara a fadar sa

KU KARANTA: Buhari ya yaudari talakan Najeriya - Tanimu Turaki

Legit.ng ta samu cewa sarautar ta Wazilin Ilori dama a hannun mahaifin sa Dakta olusola Saraki take kafin rasuwar sa.

Wani babban dan siyasa kuma jigo a jam'iyyar PDP a arewacin Najeriya dake zaman shugaban jam'iyyar a jihar Adamawa, Tahir Shehu ya bayyana mai neman tikitin takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da cewa shine kadai zai iya kayar da Buhari a zaben 2019.

Kamar dai yadda Tahir din ya bayyana, gogewa da kuma karbuwar dan takarar a dukkanin fadin kasar sune manyan abubuwan da yakama jama'a su kalla.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng