Zahra Buhari da mijinta Ahmed Indimi sun radawa yaronsu suna “Muhammad”

Zahra Buhari da mijinta Ahmed Indimi sun radawa yaronsu suna “Muhammad”

Diyar shugaban kasan Najeriya, Zahra Buhari – Indimi tare da maigidanta Ahmed Indimi sun radawa sabon jaririn da Allah ya basu.

Zahra Buhari ta haihu ne ranan 9 ga watan Yuli a kasar Andalus. Ta auri mijinta Ahmed a watan Disamban 2016.

Sirikarta ta bayyana hakan ne a shafin ra’ayi da sada zumuntarta na Instagram tare da sanya hoton taron sunan.

Zahra Buhari da mijinta Ahmed Indimi sun radawa yaronsu suna “Muhammad”
Inda akayi taron sunan

Tace: "Allah ya albarkaci danginmu fiye da tunaninmu. Kullun kara yawa mukeyi. Wani abin alfahari shine suna “Muhammad” suna da mai alfarma. Sunan mahaifina Muhammad kuma sunan yaron Muhammad. Sunan dan uwana ma Muhammad. Amma wani abin dadi shine na yar uwata wacce matar Muhammad (Ahmed) ce, diyar Muhammad ce, sirikar Muhammad ce, kuma mahaifiyar Muhammad!"

Legit.ng ta kawo muku rahoton haihuwar diyar shugaba Buhari, Zahra Buhari, wacce aka daura aurenta a birnin tarayya Abuja a shekarar 2016.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng