Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun far ma kauyen Malikawa a jihar Zamfara

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun far ma kauyen Malikawa a jihar Zamfara

Rahoton da muke smau yanzun nan na nuna cewa yan bindiga sun kai farmaki kauyen Malikawa a Gidan Gog, karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

A lokacin da muka samu wannan rahoto, yan bindigan suna kan kashe mutane yayinda suka shiga kauyen suna harbin kan mai uwa da wabi.

Kungiyar Amnesty International ta bayyana hakan a shafin sada zumuntar cewa: "Ana kan kai hari yanzu a Malikawa da ke Gidan Goga, karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara. Yan bindiga sun shiga kauyen suna harbi."

KU KARANTA: An damke yan Boko Haram 8 da sukayi garkuwa da yan matan Chibok

A watan Mayu, yan bindigan sun hallaka akalla mutane 30 a kauyen Malikawan da wannan abu ke faruwa yau. Tun lokacin, mutan kauyen sun kasance cikin fargaba.

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun far ma kauyen Malikawa a jihar Zamfara

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun far ma kauyen Malikawa a jihar Zamfara

A bangare guda, Hukumar yan sandan jihar Zamfara ta bayyana irin nasarar da ta samu wajen kawar da wani mumunan hari da yan bindiga suka kai garin Tangaram, karamar hukumar Anka a jihar Zamfara.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Muhammad Shehu, ya bayyana hakan ne a ranan Talata, 17 ga watan Yuli, 2018.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel