Zabukan 2019: Jerin gwamnonin Arewa 5 da ka iya faduwa zaben 2019

Zabukan 2019: Jerin gwamnonin Arewa 5 da ka iya faduwa zaben 2019

- Yayin da zabukan shekarar 2019 ke ta kara karatowa, yanyin siyarar na ta kara daukar zafi a dukkan fadin kasar musamman ma a yankin mu na Arewacin Najeriya.

- A bisa al'ada dai, dukkan gwamnan da ke kan yin wa'adin mulkin sa na farko yakan sake neman tsayawa takarar domin yin wa'adin mulki na biyu a kasar.

Ga dai jerin wasu gwamnonin kasar nan a yankin Arewa da masu fashin baki da tsokaci a kan al'amurran yau da kullum suke ganin da wuya su sake lashe zaben su a 2019 din saboda dalilai da dama.

Zabukan 2019: Jerin gwamnonin Arewa 5 da ka iya faduwa zaben 2019

Zabukan 2019: Jerin gwamnonin Arewa 5 da ka iya faduwa zaben 2019

KU KARANTA: An hana kafa allon kamfe din Dankwambo a jihar Adamawa

1. Abdullahi Umar Ganduje daga jihar Kano: Shi dai Ganduje ana tunanin sabanin sa da tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso zai iya kawo masa cikas a siyasar jihar.

2. Abubakar Badaru daga jihar Jigawa: Ana ganin saboda yadda 'yan adawa da tsohon gwamnan jihar Sule Lamido ke jagoranta ke da matukar karfi, za su iya kayar da shi.

3. Yahaya Bello daga jihar Kogi: Shi ma dai karfin 'yan adawar dake a jihar ne ake tunanin zai iya bashi matsala.

4. Samuel Ortom daga jihar Benue: Shi kuma wannan gwamnan kashe-kashen da ake ta fama da shi a jihar ne ake tunanin zai bashi matsala.

5. Nasiru El-rufai. Daga jihar Kaduna: Shi ma dai ana ganin duk da zaman sa dan lele a wurin shugaban kasa, 'yan adawa a jihar za su iya bashi mamaki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel