Namu ya samu: Bankin duniya ya ba wani matashi dan Arewa babban mukami
Babban bankin duniya ya nada wani matashi mai suna Muhammad Abdullahi dake zaman kwamishinan tsare-tsare da kuma kasafin kudin gwamnatin jihar Kaduna a matsayin mamaba a majalisar ta mu'amala da mutane watau Expert Advisory Council on citizen engagement a turance.
Kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta DailyNigerian, Mista Muhammadu Abdullahi, kwararre ne a harkokin tattalin arziki kuma yanzu zai hadu ne da wasu mutane biyar daga sassa daban-daban na duniya domin yin aikin.
KU KARANTA: Rahama Sadau ta sake zafafan hotuna a dandalin zumunta
Legit.ng ta samu haka zalika cewa a cikin takardar nadin ta sa, babban bankin yayi ta kwararawa matashin yabo tare da zayyano kwarewar sa da ta sa ya samu nadin.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Tambuwal ya yi tsokaci tare da tambihi mai daukar hankali a game da kashe-kashen da ke aukuwa a kusan dukkan sassan kasar nan inda ya bayyana cewa ba abun da talakawan kasar suka zaba ba kenan a shekarar 2015.
Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake nuna alhinin sa akan mutane sama da 30 da wasu 'yan bindiga suka kashe a kauyen karamar hukumar Rabbah ta jihar Sokoto.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng