Ka binciki yan sanda kan harin Fayose – Sanatocin PDP ga Buhari
Sanatocin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 12 ga watan Yuli sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kafa kungiyar masu jari’a da za su binciki yan sanda kan cin zarafin gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose da ake zargin sun yi.
Sanatocin sun yi ikirarin cewa yan sandan sun keta haddin dokar kariyar na gwamnoni masu mulki lokacin da suka kai hari ga Gwamna ayose a gangamin PDP wanda aka gudanar a ranar 11 ga watan Yuli.
Godswill Akpabio, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom sannan sanata mai wakiltan Akwa Ibem North-West, wanda yayi Magana a madadin sanatocin PDP ya bukaci gwamnatin shugaba Buhari da ta yi adalci a zaben ranar Asabar, 14 ga watan Yuli.
Akpabion ya bayyana cewa yin zabe na adalci a ranar Asabar zai daukaka martabar gwamnatin tarayya da Najeriya a matsayin kasar damokradiya.
KU KARANTA KUMA: Dambazau ya kaddamar da yaki da yan bindiga bayan harin da aka kai kauyukan Sokoto
A halin da ake ciki, Wani Jirgin sama mai saukar ungulu ya sauka a sabon gidan gwamnati, Ayoba Villa, Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.
Jirgin ya sauka ne a gidan gwamnatin jihar da ranan nan. Ana zargin cewa jirgin mai saukar ungulu ya kawo kudade ne gana wani gwamnan Kudu maso kudu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng