Budurwa mai Digiri 2 mai shekaru 40 ta kashe kanta a saboda an dame ta tayi aure

Budurwa mai Digiri 2 mai shekaru 40 ta kashe kanta a saboda an dame ta tayi aure

- Duk da zurfin karatunta amma ta sheke kanta har lahira

- A wani mataki mai kama da na yadda kwallon mangwaro na huta da kuda

Budurwar ta yi hakanne bisa takura mata sai tayi aure da aka yi a gida

Budurwar mai kimanin shekaru 40 da haihuwa mazauniyar jihar Delta ta yanke hukuncin kashe kan na ta ne, bayan matsin lambar da ta ke fuskanta daga danginta akan sai ta yi aure.

Budurwa ta kashe kanta akan matsin lambar da ta ke fuskanta daga iyayenta kan dole tayi aure
Budurwa ta kashe kanta akan matsin lambar da ta ke fuskanta daga iyayenta kan dole tayi aure

Tun da farko an samu labarin mutuwar wannan budurwa mai suna Blessing ne ta shafin wani abokinta mai suna Seeing Obajolu a dandalin sada zumunta na facebook.

KU KARANTA: Ayya: wasu ‘yan sanda 2 da wasu mutane uku sun sheka lahira a jihar Rivers

Wata majiya ta rawaito cewa budurwa tana da karatun digiri na biyu wato Mastas, wanda kuma ta kai kimanin shekaru 40 da haihuwa ba tare da ta taba yin aure ba.

Har ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa daga rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Delt, domin tabbatar da faruwar lamarin.

Mata da yawa dai na fuskantar takura daga danginta musamman iyaye mutukar suka dade ba tare da yin aure ba, sai dai irin wannan yafi faruwa a arewacin Najeriya, wanda faruwar abin a yankin kudan kasar ya zamto bazata, sakamakon da 'yan matansu kan dade kafin yin aure.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng