Ayya: wasu ‘yan sanda 2 da wasu mutane uku sun sheka lahira a jihar Rivers

Ayya: wasu ‘yan sanda 2 da wasu mutane uku sun sheka lahira a jihar Rivers

- Aran gamar 'yan sanda da wasu 'yan bindiga ya jawo mutuwar mutane 5

- A kwanan baya ma dai wasu 'yan bindiga haka siddan suka harbe wasu 'yan sanda 7 har lahira

- Har ya zuwa yanzu dai babu rahotan kama wadanda suka aikata danyan aikin

Wasu jami'an 'yan sanda guda biyu da wasa 'yan bidiga 3 sun rasa rayukansu a wani artabu da ya kaure a yankin Ozuoba dake karamar hukumar Obio/Akpor a jihar Rivers.

Ayya: wasu ‘yan sanda 2 da wasu mutane uku sun sheka lahira a jihar Rivers
Ayya: wasu ‘yan sanda 2 da wasu mutane uku sun sheka lahira a jihar Rivers
Asali: Depositphotos

Jaridar Daily Sun ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar talata, a yayin da jami'an ke bakin aikinsu na suntirin bincike na yau da kullum wanda a sanadin hakan 'yan sanda biyu suka rasa rayukansu.

Kakakin hukumar yan sanda na jihar, Nnamdi Omoni ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Laraba yayin ganawa da manema labarai a garin Fatakwal.

Omoni ya bayyana lamarin da cewa abu ne mara dadi kuma daya daga cikin 'yan bidigar shi ma ya rasa ransa a yayin batakashin.

KU KARANTA: Kashe-kashe: Ku kara hakuri hukumomin tsaro na suna aiki tukuru – in ji Buhari

Ya kara da cewa yan bidigar sun budewa yan sandan wuta ne a yayin da suke bakin aikinsu akan titi domin yin bincike inda daga bisani suka yi gaba da bindigoginsu.

Sai dai daya daga cikin jami'an yan sandan yayi nasara harbe daya daga cikin yan bidigar a yayin da suke yunkurin guduwa.

Mai magana da yawun hukumar yace shugaban hukumar yan sanda na jihar ta Rivers Zaki Ahmed, ya bayar da umarnin yin bincike domin gano su wane suka aikata wannan al'amari.

A cigaba da wani bincken kuma da ake, an samu gawar wan mutum mai suna Samuel Worgu a wani daji dake yankin Omodioga. Daily Sun ta rawaito cewa an samu gawar ne cikin yanayi na sara daban-daban a jikinta, kuma da alamun an gudu ne da motar mamacin.

Kamar yadda wani mazaunin yankin ya bayyana, yace kafin a kashe mutumin ya keto a guje cikin neman dauki a wannan halin ne ya kira dan uwansa domin ya bayyana masa halin da yake ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng