Hukumar kwastam ta yi ram da babbar mota dauke da harsasai 200,000 da ta nufi Onitsha
Hukumar kwastam ta Najeriya, shiyar jihar Neja, Kwara da Kogi ta damke wata babbar mota da nufi Onitsha dauke da harsasai 200,000 da aka shigo da su daga kasar Benin.
Mutane biyu da aka damke da wadannan harsasai sune direban motan, Bukari Dauda, da kuma mammalakin harsasan, Martin Anokwara da mota kirar Iveco mai lambar Legas AKD 904 XE.
Wadannan mutane biyu su shiga hannun jami’an kwastam ne a jihar Neja.
Game da cewar kwantrolan jihar, Benjamin Binga, yan fasa kwabrin sun shigo Najeriya ne ta iyakan Babana misalin karfe 3 na daren ranan Lahadi.
Ya ce sun wayance ne da daukan jarkoki amma bayan binciken abubuwan da ke ciki, an gano dubunnan harsasai.
A cewarsa: “Babu wanda ya sanar da damu, kawai tsananin bincike ne da jami’ai na sukayi suka gano cewa ashe akwai harsasai a kasan motocin.”
“Harsasai dubunnai ne, zamu dauki babban lokaci idan mukace zamu kirgasy. A yanzu haka muna bincike kan don me aka shigo da wadanan harsasai kuma waye ainihin mai su.”
KU KARANTA: Gwamnonin Arewa 3 da suke hanyan komawa PDP
Yayinda ake gudanar da bincike, direban mai suna, Bukari Dauda, ya ce shi dan Kotono. Dayan mutumin ya daukesa aikin tuka ne kawai zuwa Onitsha.
Ya kara da cewa shi bai san harsasai bane a ciki.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng