Takaitacen Tarihin Marigayi Adamu Ciroma wanda yayi Minista 4 a Najeriya
Mun kawo maku takaitaccen tarihin tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya na CBN watau Malam Adamu Ciroma wanda ya cika yau dinnan yana da shekaru sama da 80 a Duniya. An haifi Adamu Ciroma ne a Garin Potiskum da ke Jihar Yobe a 1934.
1. Gwamnan CBN
Adamu Ciroma yayi Gwamnan babban bankin Najeriya watau CBN daga 1975 zuwa shekarar 1977. Ciroma yayi Gwamnan ne na shekaru kusan 2 bayan Clement Isong lokacin Obasanjo yana mulkin Soja.
2. Takarar Shugaban kasa
Malam Adamu Ciroma ya nemi takarar Shugaban kasa a karkashin Jamiyyar NPN a 1979. Ciroma ya zo na 3 ne a zaben fitar da gwani inda ya zo bayan Shehu Shagari da kuma Maitama Sule. Shagari ya lashe zabe.
KU KARANTA:
3. Minista a Gwamnatin Shagari
Marigayi Adamu Ciroma ya rike Ministoci da dama a lokacin Shagari. Ciroma ya rike Ministan noma da na tattali da kuma na Masana’antu. Bayan lashe zaben Shagari karo na biyu yana cikin wadanda su ka yi ruwa-da-tsaki.
4. Minista a Gwamnatin Obasanjo
Adamu Ciroma wanda yana daga cikin wadanda su ka kafa Jam’iyyar PDP ya rike Ministan tattalin arziki a Gwamnatin Obasanjo. Bayan 2003 ne Obasnajo ya canza Ciroma a matsayin Ministar kudi da Ngozi Okonjo Iweala.
5. Jami’ar Ahmadu Bello
Adamu Ciroma yayi karatu ne a Jami’ar Ibadan bayan yayi Sakandare a Makarantar Barewa ta Zariya. Sai dai har lokacin rasuwar sa yana cikin manyan Jami’ar Ahmadu Bello da ke Garin Zariya a Jihar Kaduna.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng