Amfanin Aya ga lafiyar jikin dan Adam
Idan har yanzu ka na kokwanton amfani da aya, to ya zama lallai ka karanta wannan makalar don samun bayanai game da aya, amfaninta da illolinta.
Aya wata 'yar itace ce da ke da girma a bangaren arewacin duniya inda ake samun yanayi mabambanta. Amma a zamanin yau ta samu shuhura a Turai.
Aya tana da dandano mai gardi kuma ta yi kama da kwakwa amma ta dan fi kwakwa zaki.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Saraki ya isa jihar Plateau
Alfanun noman aya shi ne, in dai ana kula da ita, tana bayar da amfani mai kyau, bayan haka kuma tana karawa kasar da aka shuka ta albarka.
1. Tana dauke da sinadaran magnesium da calcium da kuma iron.
2. Tana samarwa da jiki sinadarin protein da kuma lafiyayen kitse.
3. Tana kunshe da sinadarin vitamin B wanda ya ke amfanar da fata da gashi da kuma farata. Don samarwa da jiki sinadaran vitamin da minerals, ya na da kyau a rika cin gram 70 zuwa 50 na aya a kullum.
4. Aya tana da amfani saboda tana kara karfin garkuwar jiki.
5. Aya na inganta yanayin da mutum ke ciki, tana tsawaita kuruciya, tana karfafa yanayin gudanar jini sannan tana kara kuzari na zahiri da na boye.
6. Haka kuma tana da amfani ga sha'anin da ya shafi ciki da hanji, tana dauke da sinadarin da ke hana cushewar ciki da kuma kumburi.
7. Har ila yau tana taimakawa wajen rage sinadarin kwalestaral mara kyau a cikin jini.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa ko Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng