Rikicin jihar Plateau: An sanya dokar ta baci a jihar Plateau
- Jihar Plateau na fuskantar barazanar barkewar rikici
- Rikicin ya fara ne da karamar hukuma daya amma yanzu sun zama uku
- Dokar hana zirga-zirgar zata ke aiki ne daga 6pm na yamma zuwa 6am na safe
Gwamnatin jihar Plateau ta sanya dukar hana zirga-zirga daga magariba zuwa asuba a kananan hukumomi uku na jihar biyo bayan yaduwar rikici daga karamar hukumar Barikin Ladi zuwa Jos ta kudu da yammacin yau Lahadi.
Hakan na fitowa a wani jawabi da sakataren gwamnatin jihar ya fitar dake bayanin cewa sanya dokar hana zirga-zirgar don kiyaye sake rasa ruyukan jama’a ne.
Ya zuwa yanzu da fara rikicin rundunar ‘yan sanda ta jihar ta bayyana cewar mutane 11 ne suka rasa rayukansu a sakamakon rikicin da ya afku a kauyukan Razat, Ruku, Nyarr, Kura da Gana-Ropp dake yankin Gashish a karamar hukumar Barkin Ladi.
KU KARANTA: Da dumi-dumi: Shugaban taron jam’iyyar APC ya matsa layar zana yayin da ake jiran ya sanar da sakamakon zaben da aka kammala
Daga baya rikicin ya yadu zuwa yankin Daffo da Kuba dake karamar hukumar Bokkos.
Rikicin ya samo asali ne tun a ranar Asabar tun bayan da wadansu da ake kyautata zaton makiyaye suka kai wasu kauyuka inda suka kashe mutane 11.
Hakan ta sanya wadansu suka fara zanga-zangar kin amincewa daga bisani suka dauki doka a hannunsu inda suka tare babbar hanyar Jos suna dukan motoci wanda hakan yayi sandiyyar haddasa haddura ga matafiya hanyar.
Dokar dai za tayi aiki daga yau da misalin 6pm na yammaci inda kowa zai shiga gidansa ba tare da ya leko ba har zuwa 6am na safe, sai dai kawai wadanda suke aiki na musamman mai muhimmanci.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar Terna Tyopev ya tabbatar da faruwar gudanar da zanga-zagar a wani sakon karta kwana, amma ya bayyana cewa an aike da jami ‘an ‘yan san don shawo kan matsalar.
Gwamnan jihar Simon Lalong da yake wurin taron zaben shugaban jam’iyyar APC na kasa yayin al’amarin ya afku, yayi saurin katse halartar taron domin dawowa gida don fara lissafin yadda za’a shawo kan matsalar. Kamar yadda wani jawabin da ya fito daga kwamishinan yada labaran jihar Yakubu Dati.
Gwamna Lalong ya bukaci jami’an tsaro a jihar da su ribanya kokarinsu don ganin an magance yawaitar kai hare-hare da ake yi kauyuka a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng