Madallah: An amince musulman lauyoyi mata za su fara sa hijabi a lokacin rantsuwa a Najeriya
Labarin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa hukumar dake kula da harkokin lauyoyi a Najeriya ta gayyaci Firdausi Amasa, lauya mace musulma da ta dage sai ta sa hijab rantsuwar su ta lauyoyi.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar nan mai rajin kare hakkin musulman Najeriya ta MURIC ta fitar inda ta bayyana jin dadin ta game da hakan.
KU KARANTA: Tsohon minista lokacin Sardauna ya rasu
Legit.ng ta samu cewa kungiyar ta MURIC ta kuma godewa Allah da ma dukkan sauran 'yan Najeriya musamman musulmai da suka dage da addu'o'i domin samun nasara akan lamarin.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa anyi ta cece-kuce a kwanan baya lokacin da aka hana Firdausi Amasa yin rantsuwar zama lauya a Najeriya saboda kawai ta sa hijabi.
A wani labarin kuma, Gamammiyar kungiyar kiristocin Najeriya 'yan asalin Arewa da ke da mambobin ta a dukkan jahohin yankin 19 sun yi tofin Allah-tsine ga hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari mai suna Lauretta Onochie.
Kungiyar dai ta ce abun takaici ne yadda hadimar tayi anfani da kalamai munana ga 'ya'yan kungiyar inda ta siffanta su da 'tsutsotsi' a shafin ta na sadarwar zamani ta Tuwita.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng