Dangote ya kaddamar da rukunin gidaje 200 da ya ginawa ‘yan gudun hijira a Maiduguri, duba hotunan
A jiya, Litinin, ne shugaban rukunin masana’antun Dangote, Aliko Dangote, ya kaddamar da rukunin gidaje 200 na farko da gidauniyar Dangote ta ginawa mazauna sansanin ‘yan gudun hijira dake Maiduri, jihar Borno.
Tun a jiya ne Legit.ng ta kawo maku labarin cewar, hamshakin attajiri Aliko Dangote ya kaddamar da wasu sabbin gidaje guda 200 da ya gina ma yan gudun hijira, musamman matan da suka rasa mazajensu a hannun Boko Haram, da kuma kananan yara da rikicin ya mayar dasu marayu.
DUBA WANNAN: Abinda kasar Amurka ta fada a kan harin da 'yan Boko Haram suka kai garin Damboa a jihar Borno
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito kimanin shekaru biyu da suka gabata ne Dangote yayi wannan alkawari, inda ya cika shi a yanzu, kamar yadda ya bayyana a ranar Litinin, 18 ga watan Yuni a jihar Borno a yayin kaddamar da gidajen.
“A shekaru biyu da suka wuce na dauki wannan alkawari a yayin wata ziyara da na kai sansanin yan gudun hijira, manufar wannan abin alheri shi ne don tallafa ma kokarin da gwamnati ke yi na sake gina ma yan gudun hijira gidajensu da yan Boko Haram suka lalata"' a cewar Dangote
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng