Wani karamin Yaro ya gamu da ajalinsa a cikin wani Kududdufi a jihar Kano
Wani karamin Yaro mai shekaru 13, Usman Faisal ya gamu da ajalinsa a cikin wani kududdufi yayin da yake wanka a cikinsa, kamar yadda kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a kauyen Gadam dake cikin karamar hukumar Ungogo na jihar Kano, inji Kaakakin hukumar kwana kwana na jihar, Saidu Mohammed.
KU KARANTA: Masha Allah: Buhari ya bullo da hanyoyi 6 na kawo karshen kashe kashe tsakanin Manoma da Makiyaya
Saidu yace lamarin ya faru ne da safiyar Talata, 19 ga watan Yuni; “Mun samu labarin tsintar gawar wani karamin Yaro a cikin wani kududdufi da misaln karf 9:10, daga bakin wani matashi Haruna Hamza inda ba tare da bata lokaci ba muka tura jami’anmu.
“Da isarsu suka tunjuma cikin wannan Kududdufi, inda suka dauko gawar wannan yaro mai suna Faisal, sa’annan suka mika gawar zuwa ga dagacin Dandishe, Alhaji Salisu Mustapha don ayi masa sutura, tare da jana’aiza.” Inji shi.
Daga karshe Kaakaki Saidu yayi kira ga iyaye dasu ja hankalin yayansu daga zuwa wankan Rafi, Tafki ko Kududdufi a wannan lokaci na damuna, don gudun kamuwa da muggan cututtuka ko kuma cin ruwa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng