Takarar Gwamna:Kwace goruba a hannun kuturu ba zai yi wuya ba – Inji Kabiru Marafa

Takarar Gwamna:Kwace goruba a hannun kuturu ba zai yi wuya ba – Inji Kabiru Marafa

Wakilin al’ummar jihar Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana kwadayinsa a fili don ganin ya dare kujerar gwamnan jihar Zamfara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Marafa ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara da shuwagabannin jam’iyyar APC na jihar Zamfara suka kai masa a gidansa dake garin Yandoton-Daji dake cikin karamar hukumar Tsafe don murnan bikin Sallah.

KU KARANTA: Kaico! Yan bindiga a jihar Zamfara sun guntule ma wani mutumi hannu

A jawabinsa, Marafa ya tabbatar musu da sha’awarsa na yin dare dare a kujerar gwamnan jihar Zamfara, inda yace nan da bada jimawa ba zai bayyana manufarsa a fili, a gaban dukkanin masu ruwa da tsaki a siyasar jihar.

Takarar Gwamna:Kwace goruba a hannun kuturu ba zai yi wuya ba – Inji Kabiru Marafa
Kabiru Marafa

Sai dai siyasar jihar Zamfara na neman rincabewa sakamakon cewa tsohon gwamnan jihar, Aliyu Shinkafi ya koma jam’iyyar APC, wanda masana siyasar jihar ke ganin gwamnan jihar Abdul Aziz Yari ne ya janyo shi don ya bashi takarar gwamnan don ganin sun kawar da tsohon gwamna, Ahmed Sani Yariman Bakura a siyasance.

A wani labarin kuma rundunar Sojin sama ta fara luguden wuta akan yan bindiga da suka addabi jama’an jihar Zamfara da kashe kashe, sace sace tare da kona musu gidaje da amfanin gona.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng