Kalli mai shari’a Adebukola Banjoko wacce ta yankewa tsoffin gwamnoni 2 masu ji da iko hukuncin zaman gidan kurkuku na shekara 28
Adebukola Banjoko shine sunan mai shari’an nan da ta kafa tarihi na adalci da kuma rashin tsoro a kotun Najeriya.
A abunda za’a kira rashin tsoro da jarumta, Mai shari’a Adebukola Banjoko tayi nasarar yanke shari’’a tare da tura tsoffin gwamnoni biyu gidan yari: Jolly Nyame, tsohon gwamnan jihar Taraba, da kuma Joshua Dariye, tsohon gwamnan jihar Filato.
A ranar Laraba, 30 ga watan Mayu, mai shari’a Banjoko ta yankewa Nyame hukuncin shekaru 14 a gidan yari ba tare da tara ba.
An samu Nyame da aikata laifin almundana yayinda yake kan kujerar gwamnan jihar Taraba.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ce ta gurfanar dashi.
KU KARANTA KUMA: 12 ga watan Yuni: Yar Abiola, Hafsat ta ba shugaba Buhari hakuri
A ranar Talata, 12 ga watan Yuni, Mai shari’a Banjoko ta sake yanke wani hukunci. Inda ta yankewa Joshua Dariye, tsohon gwamnan jihar Filato shekara 14 a gidan yari.
Shima dai ana tuhumar sa ne da almundanar kudin jama’a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin samun ingantattun labarai, bide mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng