Yanzu-yanzu: An sake sace mutane 23 a Birnin-gwari – Idon shaida

Yanzu-yanzu: An sake sace mutane 23 a Birnin-gwari – Idon shaida

Yan bindiga sun kuma garkuwa da akalla mutane matafiya 23 a hanyar Birnin-gwari, jihar Kaduna a yau Juma’a, 8 ga watan Yuni, 2018.

Daga cikin wadanda akayi garkuwa da su shine wata mata da yaronta, cewar Mohammed Kebi.

Direban, Mr Mohammed Kebi, wanda ya sha da kyar ya bayyana cewa motoci 5 suka tare da safiyar Juma’an nan.

Yace: “Akalla motoci 5 yan bindigan suka tare a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna misalin karfe 11 na safiyar yau Juma’a. Akalla mutane 23 akayi gab da su. Wannan abu ya faru tsakanin garin Kwanar-tsauni tsakanin Udawa da Labi.”

Yanzu-yanzu: An sake sace mutane 23 a Birnin-gwari – Idon shaida
Yanzu-yanzu: An sake sace mutane 23 a Birnin-gwari – Idon shaida

Har yanzu ana sauraron jawabi daga hukumar yan sanda akan wannan sabon hari.

Birnin-Gwari a jihar Kaduna na fuskanta kashe-kashen rayuka, garkuwa da mutane da asaran dukiyoyi a shekaran nan.

Domin kawo karshen wannan abu, hukumar sojin Najeriya ta kafa sabuwar bataliya a birnin gwari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel