Dan majalisar tarayya daga jihar Jigawa ya sha da kyar a hannun masu zanga-zanga
Daruruwan fusatattun matasan Jahun sun gudanar da zanga-zanga akan Alhaji Sa’idu Miga, dan majalisan dake wakiltan mazabar Jahun da Miga a majalisar wakilai, akan wakilci mara inganci.
Sun gudanar da zanga-zangan ne a lokacin da shugaban gwamnonin Najeriya, Gwamna AbdulAziz Yari, ke kaddamar da hanyar garin Jahun mai tsawon kilomita 6.5 a hedkwatar karamar hukumar Jahun dake jihar Jigawa.
An gina hanyar garin Jahun din mai kilomita 6.5 akan kudi naira miliyan 940.
Sauran ayyukan da Gwamna Yari ya kaddamar shine hanyar Gagarawa zuwa Bosuwa main tsawon kilomita 29 akan naira biliyan 3.4.
Fusattatun matasan na ta ihun ‘bama yi, bama yi’ yayinda suke kusantan dan majalisan, inda ya kai ga hargitsa taron, yayinda gwamnan ke jawabi.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya sha ruwan yabo a wajen Ekwaremadu saboda sanya hannu da yayi a dokar ba matasa damar takara
Ba don jami’an tsaron da suka gudu da shi ba da ya sha na jaki a hannun matasan.
Sunyi ikirarin cewa babu wani abun a zo a gani dad an majalisan yayiwa mutanen yankin tunda aka zabe shi domin ya wakilce su.
A halin da ake ciki, hukumar EFCC na cigaba da gurfanar da tsoffin gwamnonin kasar da ake zargi da aikata cin hanci da rashawa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng