Yanzu Yanzu: Yan sanda sun mamaye gidan gwamnatin Enugu saboda masu zanga-zanga
Rundunar yan sandan Najeriya sun mamaye gidan gwamnatin jihar Enugu domin hana mambobin kungiyar Biyafara kwace mulki.
Kungiyar ta BZF, karkashin jagorancin Benjamin Onwuka, sunyi yunkurin kaddamar da yancin Biyafara da kuma kwace gidan gwamnati ta karfin tuwo.
Yan kungiyar Biyafara sama da hamsin sun kai mamaya gidan da misalign karfe 7:30 na safiyar ranar Laraba, 30 ga watan Mayu, amma dai yan sanda sun ja masu birki, Guardian ta ruwaito.
A baya Legit.ng ta ruwaito cewa Gwamna David Umahi yace duk dan kasuwa a Ebonyi da yayi biyayya ga umurnin kungiyar Biyafara na zama a gida a ranar 30 ga watan Mayu zai rasa shagonsa.
KU KARAN TA KUMA: Kannywood: Ba zan taba shiga harkar siyasa ba – Ali Nuhu
Umahi wanda ya bayyana hakan a Abakaliki yayinda yake jawabi ga mutane a ranar dimokradiyyan 218 ya bayyana cewa irin wannan umurni baida gurbi a jihar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng