Hanyoyi 5 da za abi domin samun ingantacciyar lafiya a Ramadan

Hanyoyi 5 da za abi domin samun ingantacciyar lafiya a Ramadan

- Watan Ramadana wata ne da al'ummar Musulmai suke yin azumi na tsawon kwana 29 zuwa 30 daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana

- Duk da canje - canje da ake samu wurin cin abinci, mutum zai iya tambayar kanshi to ya zanyi in tabbatar da jiki na ya zauna lafiya ba tare da ciwuka da rashin lafiya sun dameni ba

Hanyoyi 5 da za abi domin samun ingantacciyar lafiya a Ramadan
Hanyoyi 5 da za abi domin samun ingantacciyar lafiya a Ramadan

Watan Ramadana wata ne da al'ummar Musulmai suke yin azumi na tsawon kwana 29 zuwa 30 daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana. Duk da canje - canje da ake samu wurin cin abinci, mutum zai iya tambayar kanshi to ya zanyi in tabbatar da jiki na ya zauna lafiya ba tare da ciwuka da rashin lafiya sun dameni ba? Da kyau, amsoshin basu da yawa sosai.

A kasa akwai hanyoyi guda biyar da za abi domin samun ingantacciyar lafiya a wannan lokacin:

DUBA WANNAN: Rikicin APC babbar dama ce ga jam'iyyar PDP - Sanata Gyunka

Yawaita Shan Ruwa:

Daga lokacin da mutum ya dauki azumi, jikin mutum yana rasa ruwa adadi mai yawa, saboda haka yana da mutukar muhimmanci mutum ya yawaita shan ruwa da yawa a lokacin buda baki, sannan kuma a dinga cin 'ya'yan itatuwa irin su kankana da dai sauran su.

Cin abinci mai kyau:

Cin abinci mai kyau yana da mutukar muhimmanci, musamman ma irin su wake, hatsi, da dai sauran abinci masu nauyi wadanda zasu iya rike cikin mutum, sannan kuma su bashi karfi sosai har zuwa lokacin buda baki.

Samun isashen bacci:

Saboda kauracewa abinci da mutum zai yi na wasu awanni, dole karfin mutum ya ragu fiye da yanda yake a da, saboda haka mutum yana bukatar samun isashen bacci.

Yin Sahur:

Ya tabbata ko a Hadisin Manzon Allah cewa yin Sahur yana da matukar muhimmanci, saboda yana bawa mutum karfi yanda ya kamata sannan kuma yana rage kishin ruwa har zuwa lokacin buda baki. Sannan kuma yana taimakawa wurin hana mutum ciye-ciye da yawa lokacin buda baki.

Banda cin hadama:

Yana da kyau mutum yaci abinci iya yanda yake so a lokacin buda baki. Hakan ya biyo bayan tsawon lokacin da mutum ya dauka bai ci abinci ba, to amma kuma hakan bai bawa mutum damar cin hadama ba, a addinance ma cin hadama haramun ne, saboda haka a guji cin abinda yafi karfin cikin mutum.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng