Kisan jami’in ofishin jakadancin Najeriya: Jami’an tsaron kasar Sudar sun yi ram da makashinsa

Kisan jami’in ofishin jakadancin Najeriya: Jami’an tsaron kasar Sudar sun yi ram da makashinsa

Hukumomin kasar Sudan sun tabbatar da kama mahalukin da ya kashe wan jami’I a ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Sudan, sai dai abin mamakin anan shi ne wannan makashin maza ba namiji bane, mace ce, kamar yadda Legit.ng ta samo rahoto.

An tsinci gawar jami’in ne mai suna Habibu Almu a gidansa dake babban birnin kasar Sudan, Khartoum a ranar Alhamis din da ta gabata, inda aka tsinci gawar malemale ta jike sharkaf da jini.

KU KARANTA: Annafsu binnafsu: Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanya mai matsanancin wahalka ga wani mutumi da ya kashe yarinya a Bauchi

Sai dai a ranar Lahadi 13 ga watan Mayu, kamfanin dillancin labaru na kasar Sudan, SUNA ta sanar da cewa:

Kisan jami’in ofishin jakadancin Najeriya: Jami’an tsaron kasar Sudar sun yi ram da makashinsa
Marigayin

“Yansandan kasar Sudan sun dsamu nasarar cafke wata mata yar kasar waje da ake zargi da kashe mamacin, inda da kanta ta tabbatar da cewa ita ta kashe shi, tare da sace wasu kayayyakinsa.”

Sai dai kamar yadda Legit.ng ta ruwaito, hukumar Yansanda ba ta sanar da takamaimen sunan matar da suka kama ba, ko kasar asalinta.

Tun bayan kisan Habibu, gwamnatin kasar Najeriya ta nuna bacin ranta, tare da yin Allah wadai da kisan jami’in, daga bisani ta dau alwashin baiwa hukumomin tsaro Sudan hadin kai a kokarinsu na zakulo wanda ya kashe Habibu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng