Asirin wata mai jiran kanti da ta sace Yankakkun Kaji na sama da Miliyan biyar ya tonu

Asirin wata mai jiran kanti da ta sace Yankakkun Kaji na sama da Miliyan biyar ya tonu

- Sata da damfara da masu aiki ke yi ga iyayen gidansu kullum kara yawaita take yi, a wannan karon ma wata 'yar aiki ce ta yi sama da fadi da kayan miliyoyin Nairori mallakar kamfanin da take yiwa aiki, amma bayan karanto mata laifinta na ta agaban alkali sai ta bayyana cewa ita fa ba ta da laifin komai

Wata mai suna Blessing Abel, mai shekaru 30 ta gurfana agaban Kotun Majistire a jihar Legas bisa zargin sace daskararru kaji katan guda, 4,000 da ƙimar ƙudinsu ta kai sama da Naira Miliyan biyar da dubu ɗari biyu (N5.2m) mallakar maigidanta.

Asirin wata mai jiran kanti da ta sace Yankakkun Kaji na sama da Miliyan biyar ya tonu
Asirin wata mai jiran kanti da ta sace Yankakkun Kaji na sama da Miliyan biyar ya tonu

Abel dai ana tuhumarta ne da laifuka har guda uku, laifin haɗin baki da sata da kuma satar takardun izini na Invoice.

Laifukan da ita Abel ɗin ta ce duk ba ta yi su ba.

Amma sai dai Ɗan sanda mai gabatar da ƙara Sufeto Ben Ekundayo ya haƙiƙance cewa wadda ake zargin ta aikata laifin ranar 13 ga watan Maris a unguwar Vitoria Garden City dake Lekki a jihar Legas.

KU KARANTA: Murna baki har kunne: Kano ta samu sabuwar Jami’a mai zaman kanta ta farko

Kayan dai mallakar kamfanin sayar da daskararrun kaji ne na Uwargida Benita Egbuchua, kuma ta samu damar satar ne bayan ta kwaikwayo takardun izini (Invoice) na gidan gonar Silver Stone da ta ke yiwa aiki ta hanyar bawa waɗanda suka siya kaya jabu yayinda ita kuma take kalmashe masu kyan.

"Sannan kuma tana zuba cinikin kamfanin a asusun ajiyarta na banki maimakon asusun kamfanin, yayinda kuma aka tambaye ta inda kuɗaɗen kayan suke, sai ta ce abokan cinikin ne basu biya ba."

Wannan laifi ne dai da ya saɓa da sashi na 287(7) da sashi na 365 da kuma sashi na 411 na kundin manyan laifuka na jihar Legas na 2015.

Asirin wata mai jiran kanti da ta sace Yankakkun Kaji na sama da Miliyan biyar ya tonu
Asirin wata mai jiran kanti da ta sace Yankakkun Kaji na sama da Miliyan biyar ya tonu

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito cewa, indai har kotu ta kama ta da aikata laifin, to hukuncin shekaru bakwai bisa sashin 287 (7) da kuma ƙarin wasu shekaru biyu na ragowar laifukan ƙarƙashin sashi na 411.

Yanzu haka dai mai shari'a Olumide Fusika ya bayar da belinta kan kuɗi Naira miliyan ɗaya tare da masu tsaya mata Mutum biyu. Ya kuma ɗaga shari'a zuwa 25 ga watan Mayu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng