Tsoho dan shekara 92 ya zama shugaban kasa

Tsoho dan shekara 92 ya zama shugaban kasa

- Tsohon firaministan kasar Malaysia, Mahathir Mohamad mai shekaru 92 ya bawa duniya mamaki bayan ya kayar da jam'iyyar dake kan mulkin kasar wadda ta kwashe tsawon shekara 60 mulkin kasar

Tsoho dan shekara 92 ya zama shugaban kasa
Tsoho dan shekara 92 ya zama shugaban kasa

Tsohon firaministan kasar Malaysia, Mahathir Mohamad mai shekaru 92 ya bawa duniya mamaki bayan ya kayar da jam'iyyar dake kan mulkin kasar wadda ta kwashe tsawon shekara 60 mulkin kasar.

Hukumar zaben kasar ta Malaysia tace hadakar jam'iyyun siyasa na Mista Mahathir sun lashe kujeru 115, wanda ya zarce kujeru 112 da suke bukata domin kafa gwamnati.

DUBA WANNAN: Trump yasha alwashin azabtar da kasar Iran

Mista Mahathir mai shekaru 92 ya kada jam'iyya mai mulki ta Barisan National wadda ta shafe fiye da shekaru 60 tana mulki.

Mahathir ya dade da yin ritaya, amma saboda zaben ya dawo domin karawa da tsohon yaronsa a siyasa, Najib Razak.

"Ba munzo domin daukar fansa bane, so muke mu dawo da doka da oda," inji Mista Mahathir.

Ya kuma ce yana fatan za'a gudanar da bikin rantsar da shi ranar Alhamis, wanda zai sanya ya zama shugaban kasa mafi yawan shekaru a duniya a wannan lokacin.

Saboda wannan nasarar, an bayyana ranakun Alhamis da Jumma'a a matsayin ranakun hutu a fadin kasar.

Wannan yakin neman zaben ya hada Mista Mahathir da tsohon yaronsa na siyasa, wato firaminista na yanzu mai ci Najib Razak.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel