Budurwa 'yar Najeriya ta fallasa wani da ya so kwanciya da ita kafin ya bata aiki

Budurwa 'yar Najeriya ta fallasa wani da ya so kwanciya da ita kafin ya bata aiki

Wata sambaleliyar budurwa mai suna Dami ta fallasa yadda ta ce wani mijin aure a Najeriya ya bukaci ta sadaukar masa da kanta ya kwanta da ita kafin ya bata aiki a kamfanin sa a kafar sada zumuntar zamani ta Tuwita.

Sambaleliyar budurwar dai ta bayar da wannan labarin ne tana kuma mai shawartar sauran 'yan uwanta mata da su maida hankali wajen neman na kansu musamman ma sana'a domin kaucewa fadawa irin tarkon maza da ta ce ta fada.

Budurwa 'yar Najeriya ta fallasa wani da ya so kwanciya da ita kafin ya bata aiki
Budurwa 'yar Najeriya ta fallasa wani da ya so kwanciya da ita kafin ya bata aiki

KU KARANTA: Yamutsi bayan da gwaggwon biri ya biyo manomi gida a Kuros Ribas

Legit.ng ta samu cewa a cikin wasu hotunan firar da suka yi, ta nuna cewa namijin mai suna Yemi Adewale ya bukaci da ta je ta same shi a bakin hanya ita kadai domin su kebe inda shi kuma yayi mata alkawarin aiki ba ma tare da ta bi dukkan hanyoyin da aka shimfida ba.

Budurwa 'yar Najeriya ta fallasa wani da ya so kwanciya da ita kafin ya bata aiki
Budurwa 'yar Najeriya ta fallasa wani da ya so kwanciya da ita kafin ya bata aiki

A wani labarin kuma, Babban shahararren wanda yanzu haka ake zargi da satar mutanen nan watau Chukwudumeme Onwuamadike da aka fi sani da Evans, a ranar Litinin din da ta gabata ya bayyanawa kotu cikin kuka cewar yana fa rayuwa cikin matsanancin kuci a kurkuku.

Evans wanda yanzu haka yake fuskantar shari'a a gaban babbar kotun tarayya dake a garin Legas ya ayyanawa alkalin cewa yanzu dai masu tsaron sa a gidan yarin suna muzguna masa domin suna barin sa da yunwa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel