Jami'an 'yan sanda sun damke babban malamin addini da laifin yin garkuwa da wani yaro
Jami'an 'yan sandan Najeriya sun sanar da samun nasarar cafke wani babban malamin addinin Kirista kuma Fasto a cocin Live By Faith dake a garin Ogbagu, na karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo mai suna Fasto Ifeanyi Nwachukwu bisa laifin satar dan shekara daya a duniya mai suna Damian Oluwa.
Haka ma dai tare da Faston, jami'an 'yan sandan sun kuma kama wani matashin mai shekaru 23 a duniya mai suna Miracle Emenekwuru duk dai da laifin na sata tare kuma da yin garkuwa da mutane.
KU KARANTA: Anyi wa ma'aikata karin albashi a jihar Gombe
Legit.ng ta samu cewa yan sandan sun ce da sun kammala cikakken bincike za su kai wadanda suke tuhumar a kotu.
A wani labarin kuma, Hukumar 'yan sanda ta jihar Kebbi sun gano makaman ne garin a kaboro, dake da iyaka da jihar Kebbi da kuma jihar zamfara.
Kwamishinan ' yan sandar jihar, Kabiru Ibrahim ya tabbatar wa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa jami'an 'yan sandan sun shiga kauyen inda suka samo makamai wanda suka hada da bindigogi masu kirar AK-47 guda 13, sai kuma wasu mugayen makamai 650 da kuma harsashi marasa lasisi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng