Zunubban jam'iyyar PDP ne ya sa Allah ya kwace mulki daga hannun ta - Bafarawa

Zunubban jam'iyyar PDP ne ya sa Allah ya kwace mulki daga hannun ta - Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma daya daga cikin jiga-jigan babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) Alhaji Attahiru Bafarawa ya bukaci daukacin 'ya'yan jam'iyyar da su koma ma Allah tare da rokon gafarar zunuban da suka aikata domin sune dalilin kubucewar mulki daga hannun su.

Alhaji Attahiru Bafarawa yayi wannan kiran ne ga dubban magoya bayan jam'iyyar da suka halarci taron ta na shiyyar Arewa ta yamma da ya gudana a garin Katsina jiya.

Zunubban jam'iyyar PDP ne ya sa Allah ya kwace mulki daga hannun ta - Bafarawa
Zunubban jam'iyyar PDP ne ya sa Allah ya kwace mulki daga hannun ta - Bafarawa

KU KARANTA: Dalilin da yasa Buhari ya kasa kama Obasanjo da Jonathan - Sagay

Legit.ng ta samu cewa sauran jiga-jigan jam'iyyar da suka halarci taron sun hada da tsaffin gwamnoni da ma masu ci yanzu da sauran masu fada aji a jam'iyyar daga dukkan sassan kasar nan.

A wani labarin kuma, Shugaban kwamitin tattaunawa da shawarwari game da yadda za'a kawo karshen cin hanci da rashawa wanda shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa watau Farfesa Sagay ya bayyana dalilan da yasa har yanzu tsaffin shugabannin Najeriya Obasanjo da Jonathan suka gagara kamawa.

Mista Farfesa Sagay ya bayyana hakan ne a yayin firar da yayi da manema labarai biyo bayan matsin lambar da gwamnatin ke samu daga 'yan Najeriya na bukatar kama tsaffin shugabannin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel