Nigerian news All categories All tags
Gwamnonin APC 5 da ake zargin zasu koma PDP kafin zaben 2019

Gwamnonin APC 5 da ake zargin zasu koma PDP kafin zaben 2019

- Ciyaman na jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus, ya bayyana cewa jam’iyyarsa na tattauna da wasu gwamnoni na jam’iyyar APC akan dawowar jam’iyyar PDP

- Secondus yace yawancinsu daga Arewa ta tsakiyar Najeriya suke, inda ya tabbatar da cewa suna hanyar dawowa jam’iyyar

- Secondus yace yanzu haka yana magana da wasu gwamnoni na Arewa maso Gashin kasar nan, a jawabinsa ga ‘yan jam’iyyar

Ciyaman na jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus, ya bayyana cewa jam’iyyarsa na tattauna da wasu gwamnoni na jam’iyyar APC akan dawowar jam’iyyar PDP. Secondus yace yawancinsu daga Arewa ta tsakiyar Najeriya suke, inda ya tabbatar da cewa suna hanyar dawowa jam’iyyar.

Secondus yace yanzu haka yana magana da wasu gwamnoni na Arewa maso Gashin kasar nan, a jawabinsa ga ‘yan jam’iyyar. Ya kara da cewa babu wani cikin gwamnoni PDP dake shirin komawa wata jam’iyya.

Gwamnonin APC 5 da ake zargin zasu koma PDP kafin zaben 2019

Gwamnonin APC 5 da ake zargin zasu koma PDP kafin zaben 2019

Jihohin dake a karkashin mulkin PDP na Arewa ta Tsakiya sun hada da jihar Binuwai, Plateau, Kogi, Nasarawa, Kaduna, da Kwara, kafin zaben 2015, lokacin da suka fadi zabe, APC ta karba. Amma gwamnoni shida na Arewa ta tsakiya sun karyata ikirarin Secondus.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnonin APC sun yasar da Oyegun, sunyi biyayya ga Buhari

1. Tanko Almakura

2. Abdulfatah Ahmed

3. Yahaya Bello

4. Samuel Ortom

5. Simon Lalong

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel