Buhari na samun rinjaye a majalisa kan rigimar da sukeyi da majalisar

Buhari na samun rinjaye a majalisa kan rigimar da sukeyi da majalisar

- A hankali Shugaba Buhari nata samun nasara a rigimarsu tsakaninsa da majalisa akan shugaban hukumar kula da tattalin arzikin kasa

- An jima anata jayayya akan tabbatar da shugaban wanda Shugaba Buhari ya gabatar da yardar mataimakinsa Yemi Osinbajo

- Hakan ya jawa wasu mutane 40 da shugaban ya gabatarwa majalisar don tabbatarsu, wadanda suka hada da mataimakan gwamnan banki da aka gabatar

A hankali Shugaba Buhari nata samun nasara a rigimarsu tsakaninsa da majalisa akan shugaban hukumar kula da tattalin arzikin kasa, Ibrahim Magu.

An jima anata jayayya akan tabbatar da shugaban wanda Shugaba Buhari ya gabatar da yardar mataimakinsa Yemi Osinbajo

Hakan ya jawa wasu mutane 40 da shugaban ya gabatarwa majalisar don tabbatarsu, wadanda suka hada da mataimakan gwamnan bankin tarayya da aka gabatar da mambobi hudu na kwamitin doka.

Haka zalika majalisar taki amincewa da wadanda shugaban kasa ya gabatar masu na hukumar kare hakkin dan adam.

Buhari na samun rinjaye a majalisa kan rigimar da sukeyi da majalisar
Buhari na samun rinjaye a majalisa kan rigimar da sukeyi da majalisar

Bayan rahoton da kwamitin Majalissar ya gabatar na shari’a wanda Sanata David Umaru (APC,Niger) ke shugabanta akan shigar Anthony Ojukwu Ofishin hukumar kare hakkin dan adam a matsayin jagora wanda shugaban kasa ya gabatar, kwamitin ya wanke Ojukwu bisa zargin da ake masa na fara aiki ba da izini ba.

KU KARANTA KUMA: 2019: Gwamnonin APC zasu gana da shugaba Buhari a yau

Mataimakin shugaban majalisar zartarwa Ike Ekweremadu, ya bayarda izinin tantance Ojukwu da wasu na kungiyar jagorancin babban bankin Najeriya, za’a tantancesu da zaran ‘yan majalisar zartarwar sun dawo daga hutun Easter.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng