Biki bidiri: Za a sake yin wani bikin kece raini na 'ya'yan Mohammed Indimi

Biki bidiri: Za a sake yin wani bikin kece raini na 'ya'yan Mohammed Indimi

Da alama dai wannan shekarar ta bukukuwan 'ya'yan shafaffu da mai ce a Najeriya domin kuwa yanzu haka ma dai har an fara shire-shiren yin wani bikin na kece-raini na 'ya'yan hamshafin attajirin nan Mohammed Indimi.

Kamar dai yadda muka samu, 'ya'yan na hamshakin mai kudin mata watau Hauwa da Meram, za'a yi shi ne a rana daya, garin Maiduguri babban birnin jihar Borno nan ba da dadewa ba.

Biki bidiri: Za a sake yin wani bikin kece raini na 'ya'yan Mohammed Indimi
Biki bidiri: Za a sake yin wani bikin kece raini na 'ya'yan Mohammed Indimi

KU KARANTA: Dan shekara 108 ya bayyana sirrin tsawon rayuwa

Legit.ng ta samu cewa haka zalika daya daga cikin matan, Hauwa za ta auri wani dan uwan tsohon shugaban kasar Najeriya ne kuma gwamnan Katsina, Marigayi Ummaru Musa 'Yar'adua.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa daya daga cikin 'ya'yan Mohammed Indimi din ne dai ya auri diyar shugaban kasar Najeriya Zahra Buhari a shekarar da ta gabata.

A wani labarin kuma, Wani tsoho dan kimanin shekaru 108 a duniya dan asalin kasar Canada mai suna Esmond Allcock ya danganta sirri daya da ya ke ganin cewa shine babban dalilin da ke sa tsawoncin rayuwa a duniya da samun mata ta gari.

Mista Esmond Allcock wanda ya gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar ta sa a watan Janairun da ya gabata ya bayyana hakan ne a garin sa na haihuwa inda kuma yake zaine na Kerrobert, Sask.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel