Wata 'yar Najeriya ta zama Ambassador a kasar Ingila

Wata 'yar Najeriya ta zama Ambassador a kasar Ingila

- Wata Mata ‘yar Najeriya, NneNne Iwuji-Eme, ta zama bakar mace ta farko da kasar Ingila ta bawa matsayin kwamishina

-NneNne Iwuji-Eme tace abun farin cikine tayi aiki Ingila

-Boris John ya tabbatar da NneNne Iwuji-Eme ta cancanci wannan aiki da aka bata

Wata 'yar Najeriya ta zama kwamishina a Ingila
Wata 'yar Najeriya ta zama kwamishina a Ingila

NneNne Iwuji-Eme, ‘yar Najeriya ce, amma mazauniyar Ingila, ta zama bakar mace ta farko da kasar Ingila ta bawa matsayin kwamishina, wadda yanzu zata wakilci kasar a Mozambique.

Jaridar UK Guardian ta ruwaito cewa NneNne Iwuji-Eme, kafin a bata wannan matsayi tayi aiki a Ofishin kasar waje na Ingila na tsawon shekaru 16, kuma zata maye gurbin Joanna Kuenssberg a watan Yuli, a matsayin babbar kwamishina.

DUBA WANNAN: Kotu zata yankewa duk wanda ya kashe musulmi hukuncin daurin rai da rai

A cikin rahoto, Iwuji-Eme tana ganin matsayin da aka bata na nuna “girmamawa da karramawa.” Ta kara da cewa “ Ina fatan bani wannan matsayi a Ingila kuma bakar mace ta farko da aka bawa zai karawa matasa masu basira kwarin gwiwa ba tare da la’akari da kalar fata ko inda suka fito ba, sannan su dage wurin cimma burinsu na samun matsayi a kasar waje. Ina shirin kara dankon zumunci tsakanin Ingila da Mozambique, wadanda dama sunada dangantaka ta bangare tattalin arzikin kasa.

Sakataren waje, Boris Johnson, lokacin da yake jawabi akan matsayin da aka bawa Iwuji-Eme, yace ta hangen nesa, kuma tanada masaniya akan aikin da kuma jarumtar da zata tafiyar da aikin. A matsayinmu na nahiya guda tareda kasashen dake tasowa ta bangaren arzikin kasa, Afirika tanada mahimmanci na hadin gwiwa.

An rawaito cewa Iwuji-Eme tayi aiki a matsayi mai kula da tattalin arziki a fannin filaye, abinci da al’amuran karkara da kuma harkar sarauta. Kafin a bata wannan matsayi, an turata kasar Brazil a matsayin Sakatare domin bada shawarwari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng