Mun sauya Jadawalin Jarrabawa domin bayar da dama ta Sallar Juma'a - WAEC

Mun sauya Jadawalin Jarrabawa domin bayar da dama ta Sallar Juma'a - WAEC

Hukumar Jarrabawar kammala makarantun sakandire na yankin Afirka ta Yamma wato WAEC, ta yi wasu kananan sauye-sauye a jadawalin gudanar da Jarrabawa na shekarar 2018 da za a fara gudanarwa karshen wannan wata na Maris.

Hakan ya bayu ne sakamakon huro wuta da kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya ta yi, inda ta kalubalanci hukumar da ta tsara jadawali mai cin karo da lokutan sallar Juma'a kamar yadda ya wakana shekaru biyu da suka gabata.

Hukumar ta tsara gudanar da jarrabawa ta darasin Chemistry a tsakanin karfe 2.00 zuwa 5.00 na yammacin ranar Juma'a 20 ga watan Afrilu. Wanda hakan zai ci karo da lokutan da musulmai suka saba gudanar da sallolin su na Juma'a a tsakanin karfe 1.00 zuwa 3.00 na ranar kowace Juma'a.

Dalibai yayin zana Jarrabawar WAEC
Dalibai yayin zana Jarrabawar WAEC

A yayin haka ne, kungiyar kare hakkin musulmi da sanadin shugaban ta Farfesa Ishaq Akintola, ya yi kaca-kaca da hukumar da cewa jadawalin ta manuniya ce ga rashin yiwa musulmai adalci a kasar nan.

Ya kara da cewa, rashin adalci ba abinda yake haifarwa face fitina, saboda haka za su dauki hukunci a hannayen su da gwamnatin kasar nan za ta ba su kyakkyawar kulawa.

KARANTA KUMA: Wani dattijo dan shekara 55 ya fyade diyar makwabcin sa har lahira a jihar Katsina

Shafin Jaridar Tribune na ranar Asabar ta yau ya ruwaito cewa, kakakin hukumar Mista Demianus Ojijeogu ya bayyana cewa, hukumar ta yi kananan sauye-sauye a jadawalin domin bayar da sarari ga musulmai na gudanar da sallolin su na Juma'a.

Jaridar ta ruwaito cewa, jarrabawar ta darasin Chemistry da aka tsara gudanar da ita a ranar Juma'a 20 ga watan Afrilu, ta koma ranar Talata 10 ga watan, yayin da jarrabawar da aka tsara gudanarwa a ranar talatar ta maye gurbin lokaci na ranar Juma'ar 20 ga wata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng