Dokan canza fasalin zabe: Buhari zai yi ganawan sirri da shugabannin majalisa da daren nan
Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya ganawa ta musamman da shugabannin majalisan dokokin tarayya da daren nan a fadar shugaban kasa.
Game da cewar majiya a fadar shugaban kasa, shugaba Buhari ya bukaci tattaunawa da yan majalisan kan rashin rattaba hannunsa kan dokan canza fasalin zabe.
A jiya shugaba Buhari ya aika wasika ga shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, kan dalilin da yasa ba zai rattaba hannu kan dokan canza fasalin zabe ba.
Shi kuma shugaban majalisan dattawa ya karanta wannan wasika jiya Talata a filin majalisa.
KU KARANTA: Gwamna Lalong ya sallami shugaban karamar hukuma kan kashe-kashe
Buhari ya bayyana cewa ya ki amincewa da dokan ne saboda kokarin canza fasalin zabe ka iya tanakudi da abinda kundin tsarin mulki ya samar na baiwa hukumar INEC karfin shirya zaben.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng