Wani lauya da aka kama shi turmi da taɓarya yana zakke ma ƙaramar yarinya ya fuskanci hukuncin Kotu
Wata babbar kotun majistri a garin Fatakwal ta bada umarnin garkame wani lauya mai shekaru 46, Kingsley Phillips a gidan Kurkuku bisa tuhumarsa da aka yi da yi ma karamar yarinya fyade.
A zaman kotun na ranar Laraba 14 ga watan Maris, kamfanin dillancin labaru NAN, ta ruwaito Alkalin Kotun, Kariba Braide ta bayyana cewa a baya tayi amfani da damarta wajen bada belin wanda ake tuhuma, ko za’a samu sulhun tsakaninsa da masu kararsa.
KU KARANTA: Yan matan Dapchi: Shugaba Buhari ya isa garin Damaturu don ganawa da iyayen yan matan
“Tunda dai an kasa samun sulhu a tsakanin masu kara da wanda ake kara, ya zama wajibi doka tayi aikinta yadda ya kamata, don haka na janye umarnin belin, ya zama dole a garkame min wanda ake kara a gidan Yaro.” Inji Alkalin.
Majiyar ta ruwaito Alkalin Kariba tana cewa ba za tayi sakacin rabuwa da aikinta ba akan mai laifi, duk da cewa ta bashi kwanaki 16 ya sulhunta da masu kararsa amma ya kasa, hakan ta sanya babban Alkalin jihar kiranta a waya yana gargadinta akan ta yi adalci a shari’ar.
Sai dai duk magiyar da lauyoyi abokan aikin Phillip suka yi na ganin an sun samar masa beli daga kotun ya ci tura, sakamakon Alkalin ta dage kai da fata. Rahotanni sun tabbatar da cewar Philip na iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai idan Kotu ta tabbatar da laifin da ake tuhumarsa akai.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng