Jiragen ruwa 12 jibge da man fetur, sauran kayayyaki sun isa tashar Legas

Jiragen ruwa 12 jibge da man fetur, sauran kayayyaki sun isa tashar Legas

Hukumar tashoshin jiragen ruwan Najeriya, NPA, ta bayyana cewa jiragen ruwa dauke da man fetur da wasu kayayyaki sun dira tashar jirgin sama a jihar Legas.

Hukumar NPA ta bayyana hakan ne a mujallar ta na kullum mai suna “Shipping Position” cewa jirage 8 daga ciki na dauke da man fetur kadai.

Saura hudun na dauke da man gas da kuma takin noma.

Jiragen ruwa 12 jibge da man fetur, sauran kayayyaki sun isa tashar Legas
Jiragen ruwa 12 jibge da man fetur, sauran kayayyaki sun isa tashar Legas

Hukumar ta kara da cewa ana sauraron zuwan wasu jirage 40 dauke da kayan man fetur, kayan abinci a tashohin Apapa da Tin-can cikin wata daya mai zuwa.

KU KARANTA: Yan majalisar dokoki sun hana biyan gwamnoni makudan kudade da sunan Fansho

“Jiragen da ake sauraro na dauke da alkama, kwantena, siga, gas, gishiri, kifi da man fetur.” Suka ce

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng