Hukumar EFCC ta gano Miliyan 102 da su kayi kafa a BOA
- EFCC ta gano wasu Miliyan 102 da aka sace ta bankin manoma
- Hukumar ta bankado kusan Naira Miliyan 300 a Kebbi da Kaduna
- Yanzu dai ana cigaba da gudanar da bincike ta Hukumar ta BOA
Mun samu labari cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta gano wasu kudi da su ka haura Naira Miliyan 100 da su ka bace a Bankin monoma na Jihar Kebbi.
Mai magana da yawun bakin Hukumar watau Wilson Uwurjaren ya bayyana cewa an karkatar da kudin da aka shirya rabawa manoman Jihar ne na wani tsarin babban bankin kasat na CBN. Yanzu dai Miliyan 102 sun dawo hannun Hukumar.
KU KARANTA: EFCC ta koma kan Shugaban APC Oyegun
EFCC ta bayyana cewa ta samu sama da Naira Miliyan 297 kenan daga ofishohin Hukumar BOA na Jihar Kebbi da kuma Jihar Kaduna. EFCC tace za ta cigaba da bakin kokarin ta na ganin ta karbe kudin Gwamnatin da aka sace a kasar.
Ana dai kukan yadda Jami’an BOA na bankin manona ke karkatar da kudin da aka ware domin aikin gona a kasar. Wasu na karbar kwangilar noma shinkafa amma sai ayi gaba da kudin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng