Ku daina rayuwar takama – Sultan ga shugabannin addini

Ku daina rayuwar takama – Sultan ga shugabannin addini

Sarkin Musulmi na kasa sannan kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar ya gargadi malaman addinin Musulunci kan tafiyar da rayuwa na takama wanda zai bata sunayensu da na mabiyansu.

Da yake Magana a Katsina wajen bude taron gasar Al-Qur’ani na kasa karo na 32, Abubakar yace abun damuwa ne yadda ake ganin wasu malamai da mabiya da yawa suna nuna dukiya ta hanyar hawa manyan motoci masu tsada da kuma bacci akan gadaje masu motsi.

Sultan wanda ya samu wakilcin sarkin Katsina Abdulmumin Kabir Usman yace rayuwa mai kyau da da’a shine abun da ake bukata daga malamai domin su zamo abun koyi ga mabiyansu.

Ku daina rayuwar takama – Sultan ga shugabannin addini
Ku daina rayuwar takama – Sultan ga shugabannin addini

A cewarsa addinin Islama addini ne da yayi koyi ga alkunya da kuma mutunta juna inda ya kara da cewa dukannin Musulmi na gari yayi koyi da koyarwan ta sannan kuma yabi tsarin ta domin samun rabauta.

KU KARANTA KUMA: 2019: Buhari na so yan Najeriya suyi magana tukuna – Gwamna Bello

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kimanin mutane 156 daga jihohi 32 da kuma birnin tarayya ne zasu kara a gasar karatun Al-Qur’ani na kasa karo na 32 wanda za a gudanar a jihar Katsina daga ranar 23 ga watan Fabrairu zuwa 3 ga watan Maris na wannan shekarar.

Shugaban kungiyar dake shirya gasar, Justis Musa Danladi Abubakar ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a jiya Laraba, 21 ga watan Fabrairu.

Ya bayyana cewa an kammala duk wani shiri domin gabatar da wannan taro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng