Zan kai Najeriya zuwa ga tudun tsira – Inji Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kai Najeriya zuwa ga tudun tsira duk da kalubalen da kasar ke ciki a yanzu.
Buhari yayi alkawarin ne a jawabinsa a wajen taron kaddamar da wani jirgin saman yaki mara matuki na rundunar sojin sama wanda akayiwa lakabi da Tsaigumi a jihar Kaduna.
Sashin labarai na fadar shugaban kasa ta bayar da kwafin jawabinsa ga manema labarai.
Shugaban kasar yace gwamnatinsa ta jajirce wajen shawo kan dukannin matsalolin yan bindiga da tsaro a kasar.
Sannan ya kuma roki yan Najeriya da su ba gwamnatinsa goyon baya don cimma wannan kudiri.
KU KARANTA KUMA: 2019: Buhari zai ci gaba – Inji babban sakataren gwamnatin tarayya
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha yace shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sake takara a zaben 2019.
Mustapha ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu inda yace: “A yanzu bamu da zabi da ya wuce shugaban kasa Muhammadu Buhari.”
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng