Rundunar Operation Lafiya Dole sun fatattaki Boko Haram daga wani lungu a Sambisa
- Sojojin Kasar nan sun budawa ‘Yan ta’adda wuta a Dajin Sambisa
- Rundunar Sojin kasa da na sama ne su ka tarfa ‘Yan Boko Haram
- Kanal Onyema Nwachukwu ya bayyanawa manema labarai wannan
Mun samu labari daga bakin Sojojin Najeriya cewa Rundunar Sojin kasar ta yi wa ‘Yan Boko Haram barna inda su ka tarwatsa wani wurin zaman su da ake kira Sabil Huda a cikin Dajin Sambisa a wani hari da aka kai kwanan nan.

Kamar yadda labarin ya zo mana, Sojojin Kasar sun yi nasarar karbe wasu kayan aikin 'Yan ta’addan wadanda su ka hada da wata motar yaki da kuma kayan aiki da su ka hada da gafaka da wayoyin salula da kuma wasu kayan da dama.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro barna a Kasar Yarbawa
Bayan nan kuma an ceto jama’a da dama da ‘Yan ta’addan su ka tsare wanda su ka hada da mata 19 da maza 27 a cikin Dajin. Kafin yanzu dai wannan wuri na cikin manyan inda 'Yan Boko Haram ke fakewa da shi a cikin Dajin Sambisa.
Sojojin sama na kasar sun hada kai ne da Sojojin kasa inda su ka yi wa ‘Yan Boko Haram ruwan wuta a Sambisa kamar yadda Kanal Nwachukwu wanda shi ne kusan babban Jami’in yada labarai na tawagar Operation lafiya Dole ya bayyana.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng