Dandalin Kannywood: Jarumi Adam A. Zango ya sha ruwan duwatsu a garin Gombe

Dandalin Kannywood: Jarumi Adam A. Zango ya sha ruwan duwatsu a garin Gombe

- Jarumi Adam A. Zango ya sha ruwan duwatsu a garin Gombe

- Laifin jarumin shi ne ya alkawarta masu zai zo ne da karfe 2:00 na rana amma bai zo ba sai wajen karfe 5:30 na yamma

Labarin da mu ke samu daga majiyar mu ta tabbatar mana da cewa shahararren dan fim din Hausa din nan na masana'antar Kannywood, fitaccen mawaki kuma, mai bayar da umurni a masana'antar watau Adam A. Zango ya sha ruwan duwatsu a garin Gombe dake a Arewa maso gabashin kasar nan.

Dandalin Kannywood: Jarumi Adam A. Zango ya sha ruwan duwatsu a garin Gombe
Dandalin Kannywood: Jarumi Adam A. Zango ya sha ruwan duwatsu a garin Gombe

KU KARANTA: Gwamnan Benue na shirin barin APC

Mun samu dai cewa Adam A. Zangon dai ya sha ruwan duwatsu ne daga masoyan sa da suka yi cincirindo suna jiran isowar sa a wani dan bikin gala da ya shirya masu a jihar amma sai bai zo ba a cikin lokaci.

Legit.ng ta samu cewa jarumin ya alkawarta masu zai zo ne da karfe 2:00 na rana amma bai zo ba sai wajen karfe 5:30 na yamma lamarin dai ko kusa bai yi wa masoyan na sa da suka dade suna jiran sa dadi ba.

Mun samu cewa hakan ne ma ya sa sukayi ta yin jifa tare da ayyana kalaman 'ba ma so' wanda hakan ne ma ya sa ba'ayi taron ba har sai idan kura ta lafa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng