Yanzu-yanzu: Kakakin tsohon shugaban kasa Babangida ya kai kansa ofishin hukumar 'yan sanda
- A ranar Lahadi ta karshen makon jiya ne mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya wallafa wata budaddiyyar wasika ga Buhari
- Hukumar 'yan sandan Najeriya ta bayyana nemansa ruwa a jallo ranar Litinin bisa zargin ya wallafa wasikar da sunan IBB kafin daga bisani tsohon shugaban kasar ya ce shine ya umarce shi ya rubuta wasikar
- Babban lauya Falana ya bayyana cewar hukumar 'yan sanda ta saba dokar kasa wajen bayyana neman kakakin IBB ruwa a jallo kamar wani mai laifi
A jiya ne hausa.legit.ng ta kawo maku rahotanni masu alaka da dambaruwar dake faruwa biyo bayan budaddiyyar wasikar da tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya aike wa shugaba Buhari.
Mun kawo maku rahoton cewar babban lauya mai rajin kare hakkin bil'adama Femi Falana ya caccaki hukumar 'yan sanda a kan bayyana neman kakakin IBB, Kassim Afegbua, ruwa a jallo kafin daga bisani mu kawo maku rahoton cewar Afegbua ya maka hukumar 'yan sanda da kafafen watsa labarai a kotu saboda bayyana shi a matsayin mutumin da ake nema ruwa a jallo tamkar wani mai laifi har ma ya nemi su biya shi biliyan N1.
DUBA WANNAN: Mai magana da yawun tsohon shugaban kasa IBB ya shigar da karar hukumar 'yan sanda da kafafen watsa labarai, ya nemi N1 biliyan
A yau, Laraba, Afegbua ya amince zai mika kansa ga shelkwatar 'yan sandan Najeriya dake Abuja, kwana biyu bayan bayyana nemansa ruwa a jallo.
A yanzu haka dai Afegbua ya isa ofishin hukumar 'yan sanda na kasa.
Ku ci gaba da kasancewa da Legit.ng domin jin yadda zata kasance tsakanin Afegbua da hukumar 'yan sandan Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng