Obasanjo ya fara bikon 'yan majallisu zuwa sabon kungiyar siyasar da ya kafa
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya fara bikon 'yan majallisu zuwa sabon kungiyar siyasa da yake jagoranta
-Wani dan majalissa ya ce kashi 80% daga cikin 'yan majalissun Najeriya suna tare da Obasanjo
Kungiyar siyasa da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya kafa ya fara janyo hankalin wasu muhimman ‘yan majalissar Najeriya.
Fusatattun ‘yan jam’iyyar PDP da na APC dake majalissar Dokoki da majalissar Dattawa sun fara tunani sauya sheka zuwa kungiyar siyasa da Obasanjo ya kafa dan samun nasara a zaben 2019 da za a gudanar.
Wani dan majalissa dokoki daga jam’iyyar APC wanda baya son a bayyana sunan sa, ya fadawa manema labaru cewa, alamomi da yawa sun nuna ‘yan majalissu da dama za su rasa tikitin takara a zaben 2019 shi yasa suka fara karkata da akalar siyasar su zuwa kungiyar Obasanjo.
KU KARANTA : Rikicin siyasar Kano: Zamu kwace kujeran Kwankwaso a 2019 - Ganduje
Dan majalissa yace, a cikin mutanen da ake sa rai za su hada kai da Obasanjo akwai tsofaffin gwamnoni, ‘yan majalisssa wakillai da Sanatoci da yawa.
Dan majalissar yace tabbas tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fara bikon su, kuma kashi 80% na ‘yan majalissar kasar suna tare da shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng