Hular kamfe din shugaba Buhari ta bayyana a zaman majalisa

Hular kamfe din shugaba Buhari ta bayyana a zaman majalisa

Awanni kaɗan bayan wasiƙar tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ta bayyana, wadda take shawartar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari akan haramcin sake tsayawa takara, hular kamfe na goyon bayan shugaban ta kuma bayyana a zaman majalisa da aka saba gudanarwa a kowane mako.

Rahotanni sun bayyana cewa, ministan sadarwa kuma shugaban kamfe na yankin Kudu maso yamma, Adebayo Shittu, shi ya dauki nauyin samar da wannan huluna mai dauke da rubutun 'ci gaba a 2019, Muhammadu/Osinbajo'.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, an miƙa wannan hulu na ne ga 'yan majalisar domin su rarrabawa ministoci da kuma dukkan waɗanda suka halarci zaman majalisar.

Hular kamfe ɗin shugaba Buhari ta bayyana a zaman majalisa
Hular kamfe ɗin shugaba Buhari ta bayyana a zaman majalisa

Legit.ng ta fahimci cewa, ministan na sadarwa yana hanƙoron tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Oyo, a ƙarƙashin tuta ta jam'iyyar APC.

KARANTA KUMA: Wani ɗan shekara 30 ya gurfana da laifin lalube a budurcin ƙaramar yarinya

A yayin haka kuma, jaridar ta ruwaito cewa, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shine ya jagorancin zaman majalisar da aka gudanar a yau laraba 24 ga watan Janairu, a fadarsa dake birnin Abuja.

Wadansu mahalarta zaman majalisar sun hadar da; sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Mallam Abba Kyari da kuma shugabar ma'iakatan gwamnatin tarayya, Misis Winifred Oyo-Ita.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng