Dandalin Kannywood: Ana zargin soyayya mai karfi a tsakanin Adam Zango da Fati Washa

Dandalin Kannywood: Ana zargin soyayya mai karfi a tsakanin Adam Zango da Fati Washa

A dan iskan nan mai kadawa maganganun dake ta yawo a bakunan jama'a dai yanzu shine irin so da kauna mai karfin gaske da a ke zargin ya shiga tsakanin fitattun jaruman nan na wasan Hausa fim a masana'antar Kannywood watau Adam Zango da Fati Washa.

Wannan dai na zuwa ne lokacin da hotunan jaruman biyu a tare cikin raha da daman gaske ke cigaba da bayyana a kafafen sada zumunta na zamani inda kasafai ake ganin su suna ta raha suna dariya.

Dandalin Kannywood: Ana zargin soyayya mai karfi a tsakanin Adam Zango da Fati Washa

Dandalin Kannywood: Ana zargin soyayya mai karfi a tsakanin Adam Zango da Fati Washa

KU KARANTA: An kama wani malamin addini da matar aure

Legit.ng haka zalika ta samu cewa masu sharhi akan al'amurran yau da kullum a masana'antar shiya fina-finan ta Kannywood sun lura da cewa yanzu fina-finan da jaruman biyu keyi a tare na ta kara yawa a kasuwanni.

Sai dai kuma duk da maganganun dake ta yawo a kan lamarin, har yanzu jaruman sun ki fito su tabbatar ko kuma su karyata batun wanda hakan ke kara darsa kokwanto a zukatan masu sha'awar fina-finan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel